Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta
cewa, shafin yada labarai na tashar tashar talabijin ta Carbonated.tv ya bayar
da rahoton cewa, kungiyar Amnesty Int. ta bayyana abin da yake faruwa a
jamhuriyar Afirka ta tsakiya a kan musulmi da cewa kisan kiyashi ne, kuma abin
kunya ne yadda duniya ta kauda idanu dangane da hakan.
Bayanin ya ci gaba da cewa, rikicin baya-bayan da ya sake barkewa a birnin Bangasu, dukkanin wadanda suka rasa rayukansu musulmi ne, bayan kisansu kuma an wawushe musu dukiya, yayin da wasu dubbai daga cikinsu suka tsere zuwa cikin Jamhuriyar dimukradiyya Congo.
Rahoton na Amnesty Int. ya ce daga lokacin fara rikicin jamhuriyar Afirka ta tsakiya a cikin shekara ta 2013 ya zuwa yanzu, fiye da musulmi dubu 6 ne aka tabbatar da an kashe su har lahira, yayin da wasu dubban daruruwa kuma suka tsere bayan an rusa ko kone gidajensu tare da wawure musu kaddarori.