Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin alalam cewa, Muhammad Bajudah shugaban bangaren dinka kyallaen ka’abah ya bayyana cewa za su anye kyallen ne kamar yadda aka saba a lokacin karatowar aikin hajji.
Jaridar saudiyyah ta Riyad ta habarta cewa, wannan mataki yana zuwa ne domin akucewa samun matsala a lokacin da aka samu cunkoson jama’a mahajata daga koina cikin fadin duniya, inda wasu sukan taba kyallen, wanda zai iya sanya ya samu matsala ko kuma ya lalace saboda yawan jama’a.
Bajudah ya ce domin kada wannan kyalle ya samu matsala ne sukan janye shi sama har tsawon mita uku, a gefe kuma mita 47, har sai bayan an kammala aikin hajji.