Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, jaridar Daily Mialo ta bayar da rahoton cewa, duk da harin da aka kaddamar a kan masallacin babbar cibiyar muuslmi ta Darul Faruq a cikin Minnesota da ke kan iyakar kasar Amurka da Canada, musulmi sun ci gaba da yin salla a farfajiya cibiyar.
Muhammad Umar shi ne babban daraktan wannan cbiya ya sheda cewa, an kai harin ne da wasu abubuwa masu tarwatsewa alokacin da suke cikin sallar asubahi, amma a cikin ikon Allah babu wanda ya rasa ransa, duk kuwa da cewa wasu bangarorin cibiyar sun rushe sakamakon hakan.
A nasu bangaren jama’ar da suke makwabtaka da wannan cibiya wadanda ba musulmi ba ne, sun nuna alhinins kana bin da ya faru, tare da bayar da shedar cewa dukkanin msuulmin ad suke a wurin suna zaune lafiya da kowa, kuma har sukan gayyaci mutanen wurin zuwa buda baki a lokaci azumin watan Ramadan.
Kyamar musulmi a kasar Amurka ta yi tsananin ne a cikin ‘yan watannin baya-bayan nan, tun daga lokacin da Donald Trump ya dare kan kujerar shugabancin kasar.