IQNA

Kananan Yara Palastinawa 400 Ne Isra’ila Ke Tsare Da Su A Gidan Kaso

22:55 - August 26, 2017
Lambar Labari: 3481835
Bangaren kasa da kasa, Rayyad Ashqar mai magana da yawun cibiyar Palastinawa mai kula da fursunonin da haramtacciyar kasar Isra’ila take tsare da su yabbayana cewa akwai kananan yara 400 da suke tsare a gidajen kason Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Ramallah cewa, Rayad Ashqar kakain bababr cibiyar da ke karkashin gwamnatin cin gishin kan Palastinawa mau kula da fursunoni Palastinawa da Isra’ila take tsare da su, ya bayyana damuwarsa dangane da halin da kananan yara suke ciki a kurekukun Isra’ila.

Ya ce yanzu haka akwai kananan yara palastinawa guda 400 da Isra’ila take tsare da su a gidajen kaso, inda ake gallaza musu tare da kuma tilasta musu amsa laifukan da ba su aikata ba.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, sau da yawa idan an sake su, a akn kafa iyayensu sharudda na hana su fitowa daga gida, da kuma hana su zuwa makaranta, kamar yadda ake haramta musu ganawa da danginsu ko kuma yin wasa da abokansu na cikin nguwa.

Rayyad Ashqar ya ce, irin wannan mataki na rashin imani da Haramtacciyar kasar Isra’ila take dauka a kan kananan yara Palastinawa, ya kan yi tasiri a kan lafiyarsu da ma hankalinsu.

3634320


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha