Hojjatol Islam Daumaki shugaban cibiyar hadin kan musulmi ta mabiya mazhabar ahlul bait (AS) ya bayyana wannan aiki da cewa, yana da matukar muhimamnci musammana wannan lokaci da al'ummar msuulmi suke bukatar hadin kai domin fuskantar muhimman kalu bale da ke a gabansu.
Ya ci gaba da cewa,a kowane lokaci musulmi suka hadu to suna iya yin amfani da wannan damar wajen aiwatar da abubuwa da da,ma da za su kawo msuu ci gaba a dukkanin bangarorinsu na rayuwa da zamantakewa.
Haka nan kuma dangane da matsayin wannan rana mai albarka, ya bayyana cewa mabiya tafarkin ahlul bait (AS) suna kallon Imam Ali (AS) a matsayin khalifan manzon Allah (SAW) kamar yadda shi manzon da kansa ya ayyna shi, wanda hadisai da dama ingantattu sun tabbatar da haka.
Ya ce yina mfani da wannan dama ta Ghadir ana da muhimamnci wajen aiwatar da wasu ayyuka da za su kara hada kan al'ummar musulmi domin yin aiki tare domin ci gaban addini ba tare da kowa ya bar fahimtarsa ba.