IQNA

Zanga-Zangar Neman Hadin kan Mabiya Addinai A Amurka

16:55 - September 11, 2017
Lambar Labari: 3481886
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani gagarumin jerin gwano domin nuna rashin amincewa da nuna wariyar launin fata ko ta addini a cikin Los Angeles a kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Daily News cewa, kimanin mutane 500 nes uka gudanar da gangamin domin nuna rashin gamsuwa da yadda ake nuna wa baki wariya musamman ma mabiya wasu addinai.

Tun kafin wannan lokacin da ana samun abubuwa da dama da suke faruwa tun bayan hawan sabuwar gwamnatin Amurka, wadda ta hau bisa taken kyamar addinin muslunci da kuma baki.

Irin wannan salon a sabuwar gwamnatin Amurka ya karfafa Amurka masu akidar kin duk wani addini da kuma bakin 'yan kasashen ketare, inda a halin yanzu masu irin wanna akida ta shugaban kasar na Amurka suna kai hari kai tsaye a kan msuulmi da wuraren ibadarsu.

Surayya Din day ace daga cikin msuulmi mazauna wannan yanki, kuma tana daga cikin wadanda suka shiga wannan jerin gwano, inda ta bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne domin nuna ma duniya cewa suna fuskantar matsala a kasar da ke da'awar cewa tana bin tsarin dimukradiyya.

Ta ce yin haka a daidai wannan lokaci da ake tunawa zagayowar harin 11 ga watan Satumba yana dauke da sakon cewa musulmi da ma wadanda ba musulmi bas u amince da ta'addanci ba, kuma bas u amince da kyakamr addinai ko baki da nuna musu wariya ba.

3640639


captcha