IQNA

Sayyid Ahmad Khatami:
22:07 - September 16, 2017
Lambar Labari: 3481902
Bangaren siyasa, Limamin da ya jagrancin sallar juma'ar birnin tehran ya ce kisan da aka yiwa al'ummar musulmi a kasar Mymmar babbar masifa ce wacce kuma ke bayan wannan ta'addanci gwamnatin haramcecciyar kasar yahudawa ce.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A yayin da yake khudubar sallar juma'a a nan birnin tehran, Ayatollah Ahmad Khatami ya bayyana cewa gwamnatin kasar Myammar na yiwa al'ummar musulmi kisan kare dangi da makaman da aka kisan musulmi a birnin gaza, kuma duk da irin wannan rashin imani na wadannan magabata, aka bayar da kyautar nobel na zaman lafiya ga jagorar gwamnati da ministan harakokin wajen kasar.

Limamin yayi kakkausar suka kan shurun da kungiyoyin kasa da kasa gami da wasu kasashen musulinci suka yi sannan ya ce wannan ta'addanci da aka yiwa musulmin kasar myammar shi ke nuna cewa addinin musulinci na kara karbuwa a duniya, lamarin da yake sanya fargaba a zukatan masu girman kai.

A yayin da ya koma kan maganar zaben raba gardama na ballewar kurdawan kasar Iraki, Ayatollah Khatami ya danganta batun da makarkashiyar kasashen yamma da gwamnatin HKI, sannan kuma ya ce goyon bayan da gwamnatin HKI ta nunawa dangane da wannan zabe shi ke nuna cewa bayan kashin da 'yan ta'addar dake samun goyon bayan gwamnatin HKI suka sha a kasashen Siriya da Iraki, yanzu kuma gwamnatin na kokarin raba kasar Iraki.

Yayin da ya koma kan kiran wasu magabatan kasar Amurka na cewa a gudanar da bincike a cibiyoyin tsaron Iran, Ayatollah Khatami ya ce cibiyoyin Tsaron Iran, sirrin al'ummar kasar ne don haka babu wata yarjejjeniya ko wani tsarin siyasa da za a bawa damar bincike a wuraren sirrin al'ummar Iran.

Har ila yau Limamin yayi alawadai kan harin ta'addancin da kungiyar is ta kai a garin Nasiriya na kasar Iraki a jiya alkhamis, lamarin da yayi sanadiyar shahadar maziyartan kasashen Iran da Iraki.

3642097


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Tehran ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: