Babbar matsalar da suke fusnkanta it ace ruwan sama wanda ke zuba kamar da bakin kwarya a cikin yankunansu da suka baria cikin kasar Myanmar, hakan nan kuma a kan hanyarsu ta zuwa kasar bangaladesh da ke makwaftaka da wurin.
Da dama daga cikinsu suna yin amfani da ledoji domin kare kansu daga ruwan sama, wanda kuma hakan baya wadatarwa, yayin da wasu kuma sukan mutu a cikin koramu da suke tsallakawa.
Yanzu haka rahotanni sun tabbatar da cewa akwai adadi mai yawa na mutanen da suka mutu a cikin koramu, wasu kuma a kan hanya sakamakon kamuwa da cututtuka ko gazawa.