Harin wanda wasu 'yan ta'adda 4 suka shirya kai shi bai yi nasara ba, bayan da jami'an tsaro suka samu bayanan sirri dangane da wannan shiri na 'yan ta'adda, inda suka kame sub a tare da sun Ankara ba.
Ya zo a cikin bayanin cewa, dakarun runduna ta 43 da kuma 6 sun samu nasarar cafke 'yan ta'adda 4 da suke hankoron kaddamar da hari kan masu gudanar da taron makoki a cikin yankin Ramilta da kuma Aziyya da suke cikin gundumar Balad a rewacin kasar Iraki.
A cikin shekaru baya-bayan na da ke gudanar da tarukan tunawa da zagayowar lokacin shahadar Imam Hussain (AS) a kasar Iraki, 'yan ta'adda na hankoron ganin sun kawo cikas ta dukkanin hanyoyi ga gudanar da wadannan taruka.