IQNA

Koyar Da Fasahar Rubutun Kur’ani A Najeriya

23:40 - October 10, 2017
Lambar Labari: 3481985
Bangaren kasa da kasa, mataimakin shugaban kungiyar masu fasaha ta kasa a Najeriya ya gana da shugaban ofishin yada al’adu na Iran a birnin Abuja.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar bunkasa al’adun muslunci ta bayar da bayanin cewa, a ganawar da ta gudana tsakanin Adamu Shehu Liman mataimakin shugaban kungiyar masu fasaha ta kasa a Najeriya da Sayyid Mahmud Azimi Nasr Abad shugaban ofishin yada al’adu na Iran a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, sun tattauna muhimamn batutuwa da suka shafi bangarorin biyu.

A zantawar ad suka yi, mataimakin shugaban kungiyar masu fasaha a Najeriya ya bayyana cewa, akwai bukatar Iran ta aike da wasu masu fasahar rubutu zuwa Najeriya, domin koyar da masu sha’awar rubutun kur’ani ta hanyar fasahar zamani a kasar.

Ya ci gaba da cewa, al’ummar musulmi na Najeriya sun jima suna yin amfani da hanyoyinsu da suk gada wajen rubutun kur’ani, amma hakan ba zai hana daukar wata fasahar ba daga wasu masanan na wata nmahiyar.

Azimi Nasr Abad ya ce nan ba da jimawa ba za a gudanar da wani baje kolin fasahar rubutun kur’ani da salon a musamman wanda masu fasahar rubutu Iraniyawa suka kirkiro tun a zamunnan da suka gabata, da ma sabbin fusahohin rubutu na zamani da ake yin aiki da su a halin yanzu.

3650782


captcha