IQNA

Taron kasa Da kasa Na Taimaka Ma Al’ummar Palastine

23:51 - October 24, 2017
Lambar Labari: 3482032
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da zama taron taimaka ma al'ummar Palastine mai take dukkaninmu zuwa Quds a birnin Idstanbul na kasar Turkiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arabi 21 cewa, an a jiya ne aka fara gudanar da zama taron taimaka ma al;ummar Palastiny mai take dukkaninmu zuwa Quds a birnin Idstanbul na kasar Turkiya tare da halartar masana daga kasashen duniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan taron yana daga cikin irin sa wanda kungiyar kare masalalcin quds ta duniya ta ke shiryawa a kasashe daban-daban.

A wannan karon taron yana samun halartar masana daga kasashe 25 na duniya da kuma mahalarta 400 da suke gabatar da kasidunsu gaban taron.

Akram Adluni shi ne babban sakataren kungiyar kare masallacin quds ya bayyana a yayin bude zaman taron cewa, babbar manufar shirya wannan taro ita ce tattauna muhimman lamurra da suka shafi masallacin quds da kuma al’ummar Palastinu.

Baya ga haka kuma a samo hanyoyina taimakon wannan al’umma da ke fuskantar zalunci da danniya tsawon shekaru daga yahudawan sahyuniya.

Sheikh Ikrama Sabri limamin masallacin aqsa ya bayyana cewa, wannan masallaci mai albarka yana fuskantar babban hadari daga yahudawa sahyuniya wadanda suke killace da shi, inda ya ce nauyi da ya rataya kan dukkanin msuulmi su kare wannan masallaci alkiblar musulmi ta farko.

3656283


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha