IQNA

An yi Rijistar Kungiyoyin Bayar Da Tallafi Dubu 7 A Karbala

19:40 - October 25, 2017
Lambar Labari: 3482036
Bangaren kasa da kasa, jami'an yan sanda a birnin Karbala mai alfarma sun sanar da cewa, ya zuwa kungiyoyi da cibiyoyi masu gudanar da ayyukan bada agaji tallafi dubu 7 ne a ka yi rijistarsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin iraqakhbar.com cewa, , jami'an yan sanda a birnin Karbala mai alfarma sun sanar da cewa, ya zuwa kungiyoyi da cibiyoyi masu gudanar da ayyukan bada agaji tallafi dubu bakawai ne a ka yi rijistarsu domin yin aikia tarukan arbaeen.

Bayanin ya ci gaba da cewa, a wannan karon an yi tsari wanda yasa ba za a samu matsaloli sosai kamar yadda aka samua lokutan baya ba, domin kuwa irin wadannan ayyuka za a gudanar ad su tare da sanya idon ofishin gundumar Karbala ne.

Dukkanin matakan da jami'an tsaro suka dauka suna da alaka ne da bayar da kariya ga miliyoyin masu ziyara daga kasashen duniya da kuma kasar ta Iraki.

Taron arbaeen dai shi ne taro mafi gima da ake gudanarwa aduniya domin ziyarar hubbaren Imam Hussain da kuma zuriyar manzon Allah da aka yi msuu kisan gilla a karbala.

Dubban Irakawa ne tare da wasu daga cikin masu ziyara suke gudanar da hidima kyauta ga miliyoyin musulmin da suke halartar wannan taro mai albarka.

3656556
captcha