Yace sun bata shekaru fiye da 30 suna ta jayayya akan akidu wanda kuma hakan ba zai taba kawo akrshe ba,a kan haka dole ne akawo karshen tsatsauran ra'ayin akida a cikin harkokin tafiyar da mulkin gidan sarautar kasar.
Kamar yadda kuam yace madadin tsatsauran ra'ayi, za su rungumi matsakaicin ra'ayi a cikin lamurransu a shekaru masu.
Sai ga dukaknin alamu wasu na da shakku kan wannan furuci da wanann matashi dan shekaru 32 ya yi, domin kuwa sa;on tsatsauran ra'ayi shi ne abin da turawan Birtaniya suka gina gidan sarautar saudiyya akansa, domin shagaltar da msuulmi da wasu kanan abubuwa su yi ta jayayya a kansu suna kafirta junansu da jifar junansu da shirka da bidi'a da sauransu, wanda kuam shi enabin da masarautar Saudiyya take yadawa a cikin kasashen musulmi.
Kamar yadda shi kansa Muhamamd Bin Salman bai fita daga hakan ba, domin kuwa yana da hannu dumu-dumua cikin kisan kiyashin da gwamnatin Saudiyya ke yia akn dubban kananna yara da mata a Yemen, kuma yana da hannu wajen taimaka ma 'yan ta'addan wahabiyawa irin su IS da makanatansu da suke yaki a Syria da wasu kasashen larabawa.