IQNA

Trump Na Son Fakewa Da Harin New York Domin Cutar Da Musulmi

22:08 - November 04, 2017
Lambar Labari: 3482066
Bangaren kasa da kasa, tun bayan kai harin birnin New York a daren Talata da ta gabata Trump yake ta kokarin yin amfani da wannan damar domin cutar da musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CAIR cewa, tun bayan kai harin birnin New York a daren Talata da ta gabata, wanda 'yan ta'addan daesh suka dauki nauyin kaddamarwa, shugaban Amurka Donald Trump yake ta kokarin yin amfani da wannan damar domin cutar da musulmi da sunan dokar hana hijira da kuma shigar msuulmi cikin Amurka.

Christina Sinha ita bababr lauya mai kare baki 'yan kasashen Asia mazauna kasar Amurka, ta bayyana cewa, abin da ya faru na kai harin New York aiki ne na ta'addanci, amma kuma hakan baya nufin cewa dukkanin musulmi 'yan ta'adda ne, kuma ba a dalci ba ne a jingina wannan hari da musulmi.

Albert Fax dan majalisar dokokin kasar Amurka ne, wanda shi ma a nasa bangaren ya bayyana cewa ayyukan ta'addanci ba za su tab azama wata hujja ta cutar da dukkanin musulmi ba, domin kuwa 'yan ta'addan da suka kai wannan harin ba su bar kowa ba, musulmi da wand aba musulmi duk kashewa suke yi.

Ya kara da cewa Trump yana son ya yi amfani da wannan damar domin ya cutar da musulmi, kuma ya samu hujjar aiwatar da dokar hana musulmi shiga Amurka, da suna yana kare Amurka daga ta'addanci, dan majalisar ya ce ba za su amince da hakan ba.

3659876


captcha