Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren hulda da
jama'a na karamin ofsihn jakadancin Iran a Senegal bayar da bayanin cewa, tawagar
wasu masana na jami'oin Iran da suka ziyarci kasar Senegal sun duba wani dakin
ajiye kayan fasahar rubutun kur'ani a Dakar fadar mulkin kasar ta Senegal.
Tawagar ta ziyarci muhimamn wurare na tarihi a wannan kasa ta Senegal daya daga cikin muhimman kasashe tafuskar addini a yammacin nahiyar Afirka.
Kasar Senegal dai tana da kyakkayawar alaka ta fuskar al'adu da ilimi da kasar Iran, wanda hakan ya bayar da damar samun musayar ra'ayi domin amfanin bangarorin biyu.
Akasarin mutanen kasar Senegal dai musulmi ne mabiya tafarkin darikun sufanci, wanda hakan ya taimaka matuka wajen samun malamai da kuma mutane masu tsoron Allah da suka jagoranci musulmin kasar bisa tafarki na koyarwar addini tsawon daruruwan shekaru a kasar.