Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Alarab ta kasar Qatar ta bayar da rahoton cewa, a jiya an fara gudanar da gasar karatu da hardar ur’ani mai tsarki ta kasa baki daya, mai taken gasar Sheikh Jasim bin Muhammad Bin Sani.
Bayanin ya ce wannan gasa an kasa zuwa bangarori biyu, da hakan ya hada da yan kasar ta Qatar da kuma musulmi mazauna kasar wadanda ba ‘yan asalin kasar ta Qatar ne ba.
Daga cikin abubuwan da gasar take mayar da hankali a kansu akwai hardar dukkanin kur’ani, sai kuma karatu na dukkanin kur’ai, baya ga haka kuma akwa hukunce-hukuncen kur’ai da kuma tafsiri.
Wannan gasa dai na daga cikin irin ta mafi girma da ake gudanarwa akasar ta Qatar, wadda kuma mafi yawan masu shiga cikinta matasa ne da kuma malaai masu koyar da karatun kur’ani a makarantun islamiyya a kasar.