IQNA

Gwamnatin Muzambik Ta Rufe Masallatai Uku

21:41 - November 29, 2017
Lambar Labari: 3482151
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Muzambik ta dauki nauyin rufe wasu masallatan musulmi guda uku a rewacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoli cewa, gwamnatin kasar Muzambik ta dauki nauyin rufe wasu masallatan musulmi guda uku a rewacin kasar sakamamon harin da wasu suka kaddamar kan jami'an 'yan sanda na kasar a kan iya da Tanzania.

Nasrullah Dul shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin msuulmia kasar ya sheda wa manema labarai cewa, wannan mataki ya zo musu da mamaki, domin kuwa wadanda suka kaddamar da hari kan jami'an tsaro ba mutanen kasar muzambik ba ne.

Ya ci gaba da cewa, musulmin kasar ab su da wata alaka da abin da ya faru, bil hasali ma suna kallon hakan ne a matsayina aikin ta'addanci, wanda suka yi Allah wadai da shi.

Ya kara da cewa suna kira ga gwamnatin Muzambik kan cewa, ta daina kallon muuslmin kasar a matsayin masu alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda, domin kuwa suna zaune da kowa lafiya, kuma suna kiyaye dokoki tare da girmama sauran al'ummomi da mabiya addinai a kasar.

Har aynzu dai babu wata kungiya da ta dauki nauyin kai harina kan 'yan sandan Muzambik, amma dai ana gain hakan baya rasa nasaba da kungiyoyin wahabiyawan 

takfiriyya.

3668240




captcha