IQNA

20:43 - December 02, 2017
Lambar Labari: 3482159
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gagarumar zanga-zangar kin jinin shugaban kasa Amurka Donald Trump a gaban ofishin jakadancin Amurka da ke London.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar press TV ta bayar da rahoton cewa, a jiya an gudanar da gagarumar zanga-zangar kin jinin shugaban kasa Amurka Donald Trump a gaban ofishin jakadancin Amurka da ke London domin nuna rashin gamsuwa da matakinsa na kin jinin usulmi.

Wannan jerin gwano kungiyoyi masu adawa da nuna wariya da banbancin kabila ko adini ne suka shirya gudanar da shi.

A ranar Laraba da ta gabata ce Trump yay i kalaman batuncia kan addinin muslunci, tare da bayyana musulmi da kuma addinin muslunci a matsayin su ne tushen ta’addanci a duniya.

Tarump ya yi wadannan kalaman ne a kan shafinsa na twitter bayan da wani dan siyasa a Birtaniya mai kiyayya da muslunc ya fitar da wani aifan bidiyo na wan matashi kirista was na azabtar da shi, inda ya danganta hakan da musulmi ba tare da wani dalili ba.

Shugaban na Amurka yay i amfani da wannan damar domin cin zarafin musulunci kamar yadda ya saba, amma ya fuskanci martani daga manyan jami’an gwamnatin Birtaniya, da suka hada har da Theresa May firayi ministan kasar, inda ita ma ya mayar mata da martania cikin izgili da cewa, ta mayar da hankali kan ta’adanci muslunci maimakon magana akansa.

3668954

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: