IQNA

16:55 - December 03, 2017
Lambar Labari: 3482162
Bangaren kasa da kasa, minister mai kula da harkokin addini a kasar Morocco ya bayyana cewa yanzu haka akwai makarantu dubu 14 na koyar da kur'ani.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadadarwa na yanar gizo na Morocco World News cewa, Ahmad Taufiq minister mai kula da harkokin addini a kasar Morocco ya bayyana cewa yanzu haka akwai makarantu dubu 14 na koyar da kur'ani a sassa na kasar.

A bayanin nasa wanda ya gabatar a wajen taron maulidin amnzon Allah (SAW) ya ci gaba da cewa, a cikin wadannan makarantu akwai dalibai kimanin dubu 450 wadanda kimanin kasha 40 cikin dari daga cikinsu mata ne.

Taifiq ya kara da cewa, baya ga wadannan makarantu an sak ebude wasu wadanda yawansu ya kai dari uku daga bisani, wadanda suma suna ci gab ada gudanar da karatu kuma yaye dalibai.

Bisa ga al'ada ta mutanen Morocco yara sukan fara karatun kur'ani kafin su shiga makarantun book, inda sukan iya karatu kafin lokacin cikar shekaru shiga firamare.

Yara daliban kur'ani sukan sauke kur'ani mai tsarki ne a shekaru na 12 – 13, wato shekarun da suke kammala karatun firamare zuwa sakandare.

Baya ga tsarin zamani da ake tafiyar da shin a koyar da karatun kur'ani, wadannan makarantu na allo har yanzu suna da tasiri wajen koyar da karatun kur'ani mai tsarki a kasar.

3669133

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: