Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na Saba'a net ya bayar da rahoton cewa, gwamnanan na San'a ya tabbatar da cewa masu yunkurin haifar da fitinar sun tsere daga wuraren da suka kafa tungarsu a cikin birnin da ma sauran birane.
Inda ya ce yanzu haka jami'an tsaro ne suke rike da dukkanin wuraren da 'yan bindiga na tsohon shugaban kasar suka mamaye a ranar Laraba da ta gabata, yayin da wasu daruruwa daga cikinsu suka mika kansu da makaman da ke hannunsu.
Rundunar sojin kasar Yemen tare da taimakon dakarun sa kai na kabilun larabawan Yemen sun samu nasarar murkushe boren da tsohon shugaban kasar ta Yemen Ali abdallah saleh ya tayar, da nufin bayar da dama ga kasashen da ke yaki da al'ummar Yemen su samu damar kwace birnin San'a, hakan yana faruwa ne tare da taimakon gwamnatocin UAE da kuma Saudiyya, amma dai lamarin bai yi nasara ba.