IQNA

16:58 - December 04, 2017
Lambar Labari: 3482167
Bangaren kasa da kasa, Jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi awon gaba da mutane hudu daga cikin masu gadin masallacin aqsa.

Jami'an Tsaron Isr'aila Sun Yi Awon Gaba Da Masu Gadin Masallacin QudsKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na kamfanin dillancin labaran Iina ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron yahudawan sahyuniya sun kame Lu'ai Abu Sa'ad, Ahmad Abu Aliya, Fadi Abu Mirz da kuma Qasim Kamal, wadanda suke gadin masallacin aqsa maia lfarma.

Rahoton ya ce bayan kame su, an nufi wani wuri da su da ba a san ko ina ne ba, kuma jami'an tsaron yahudawan ba su yi kowa karin bayani kan dalilin yin hakan ba.

Amma dai waa majiya a cikin gwamnatin Isra'ila ta bayyana cewa, an kame wadannan mutane masu gadin masallacin quds ne sakamakon matakain da suka dauka na hana wasu yahudawa shiga cikin bangaren Qubbatus sakhrah da ke cikin bangaren masallacin, da suka hada har da wasu jami'an gwamnatin Isra'ila.

3669558

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، masallacin aqsa ، mutane ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: