IQNA

Al’ummar Palastinu Sun Shiga Yajin Aiki A Dukkanin Biranansu kan Matakin Donald Trump

23:19 - December 08, 2017
Lambar Labari: 3482180
Bangaren kasa da kasa, tun bayan sanar da matakin amincewa da birnin Quds a matsayin babban birnin yahudawan Isara’ila da Donald Trump ya yi al’ummar Palastinu ke ta da gudanar gangami da zanga-zanga.

 

Kamfain dllancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na thenational ya habarta cewa, jarida Independent ta kasar Birtaiya ta bayar da rahoton cewa, tun daga jiya bayan sanar da matakin amincewa da birnin Quds a matsayin babban birnin yahudawan Isara’ila da shugaban Amurka Donald Trump ya yi al’ummar Palastinu suke ta da gudanar gangami da zanga-zanga da yajin aiki dukkanin branan Palastinu.

Jaridar Guardian ta kasar Britaniya ta rubuta cikin shafuffukanta a yau Alhamis kan cewa matakin da shugaba Trump ya dauka zai haifar da mummunan sakamako ga Amurkan da kuma kasashen Larabawa.

Jaridan ta kara da cewa dauke ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Quds zai gamu da maida martani wanda a halin yanzu ba zamu iya sawwarashi ba. 

Sai kuma jaridar Le monde ta kasar Faransa wacce ta rubuta cewa dukkan shuwagabannin kasashen Larabawa da na kasashen Turai sun yi Allah wadai da matakin da shugaba Donal Trump ya dauka na maida birnin Quds ya zama cibiyar gwamnatin HKI. 

Sai kuma jaridar Liberation ita ma ta kasar Faransa tana cewa dangane da wannan batun Daga Paris zuwa Tehran, daga Vatican zuwa Istambul, daga Brussels zuwa Alkahira dukkan shuwagabannin wadan nan kasashe sun ja kunnen Trump kan wannan matakin amma bai sauraresu ba.

3670413

 

 

captcha