IQNA

15:03 - December 13, 2017
Lambar Labari: 3482197
Bangaren kasa da kasa, Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun bude wuta kan wasu matasa biyu a yankin Zirin Gaza na Palasdinu lamarin da ya yi sanadiyyar shahadarsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kafar watsa labaran Palasdinu ta watsa labarin cewa: Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun bude wuta kan wasu matasan Palasdinawa biyu da suke kan babur a yankin Zirin Gaza lamarin da ya janyo shahadarsu a jiya Talata. 

Har ila yau jirgin saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila maras matuki ciki ya kai hari kan wasu matasan Palasdinawa a garin Baitu-Lahaya da ke shiyar arewacin Zirin Gaza, inda harin ya jikkata Palasdinawa masu yawa.

A cewar ma'aikatar lafiya ta Palasdinu tun daga ranar Juma'ar da ta gabata zuwa yanzu, Palasdinawa shida ne suka yi shahada, yayin da wasu fiye da dari uku suka jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suke ci gaba da kai wa kan al'ummar Palasdinu da suke boren nuna rashin amincewa da shelanta birnin Qudus da shugaban kasar Amurka Dinald Trump ya yi a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.   

3672232 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، palastinawa ، qudus ، zirin gaza ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: