IQNA

16:57 - December 19, 2017
Lambar Labari: 3482214
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da zaman taron makon kur'ani na kasa a kasar Aljeriya a karo na 19.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an bude zaman taron makon kur'ani na kasa a kasar Aljeriya a karo na 19 a birnin Aljiers fadar mulkin kasar Aljeriya, tare da halartar mutane fiye da 600 daga cikin da wajen kasar.

Muhammad Isa shi ne minister mai kula da harkokin addini na kasar ta Aljeriya ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na goma sha tara da suke shirya gudanar da irin wannan zaman taro na karawa juna sani a kan kur'ani mai tsarki.

Ya ce babbar manufarsu ta yi hakan ita ce kara yada lamarin kur'ani mai tsarki a tsakanin al'ummar kasar, wanda kuma yana yin gagarumin tasiri, kasantuwar cewa malamai da masana suna gabatar da jawabai wadanda ake nunawa kai tsayea  kafafen yada labarai inda al'umma suke amfana.

A wannan karon kamar sauran lokutan da suka gabata, manyan malaman kur'ani da na addini daga dukaknin lardunan kasar suna halartar taron, kamar yadda kuma masana daga jami'oi da cibiyoyi na addini da na ilimi duk sun tura wakilansu a taron.

Baya ga haka kuma wasu daga cikin jakadun kasashen musulmi a kasar ta Aljeriya suna halartar wurin, ko kuma wakilansu, wanda hakan ya mayar da taron ya zama taro na kasa da kasa.

3674078

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Aljiers ، Aljeriya ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: