IQNA

An Gudanar A Birnin Pretoria:

Taro Mai Taken Ranar Iran Tare Da Marayu A Afirka

16:59 - December 19, 2017
Lambar Labari: 3482215
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taro mai taken ranar Iran tare da marayun Afirka ta kudu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai an cibiyar yada al'adun muslunci ya habarta cewa, a jiya ne aka gudanar da wani taro mai taken ranar Iran tare da marayun Afirka ta kudu a birnin Pretoria, kamar yadda kuma an gudanar da wani taron makamancinsa a birnin Johannesburg.

Bayanin ya ci gaba da cewa marayu 100 ne suka samu halartar wannan taro wanda aka gudanar a karamin ofishin jakadancin Iran a Pretoria, da kuma a birnin na Johannesburg babban birnin kasuwanci na kasar.

Daga karshe an bayar da kyautuka ga dukkanin marayun da suka halarci wannan wuri, daga cikin abubuwan da aka basu har da tufafi da kuma littafan karatu wadanda aka rubuta a cikin harsunan turanci da kuma fassarar farisanci.

3674118

 

captcha