IQNA

An bayar Da Kyauta Mai Taken Manzon Rahma Ga Wasu mawakan Musulunci A Senegal

23:51 - December 20, 2017
Lambar Labari: 3482219
Bangaren kasa da kasa, an bayar da wasta kyauta mai taken Manzon Rahma ga wasu mawakan muslunci a Senegal.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya an gudanar da wani taro a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal, inda aka bayar da kyautuka na musamman ga wasu daga cikin fitattun mawakan muslunci masu bege ga manzon Allah (SAW).

Daga cikin mawakan akwai Abdullahi Fodi Andai, sai kuma Jibril Diallo Fami sai kuma Aisha Diop, wadanda dukkaninsu fitattun masu wakokin yabo da bege ne ga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

Sayyid Hassan Ismati shi ne shugaban ofishin kula da al'adun muslunci na kasar Iran a kasar Senegal, yana daga cikin wadanda suka halarci wannan taro.

3674614

 

captcha