IQNA

Shugaban Hamas Ya Gargadi Amurka Kan Matsayar Da Ta Dauka

22:41 - December 23, 2017
Lambar Labari: 3482229
Bangaren kasa da kasa, shugaban kungiyar Hamas Isma’il Haniyya ya gargadi Amurka dangane da matsayar da ta dauka kan batun kudus da kuma hakkin komawar Palastinawa kasarsu.

Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa, Shugaban Kungiyar Hamas Isma'il Haniyyah ya bayyana haka ne jim kadan bayan da yawancin kasashen duniya suka nuna kin amincewarsu da duk wani sauyi akan birnin Kudus.

Shugaban na kungiyar Hamas ya kara da cewa; Kasashen da suka kada kuri'ar kin yarda da sauya matsayin birnin kudus, sun bayyana matsayar al'ummu masu 'yanci ne na duniya, da kuma kin amincewa da siyasar danniya ta Amurka.

Bugu da kari, Haniyyah ya kira yi Amurka da ta girmama bukatun al'ummun duniya ta janye daga matsayinta na daukar Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Kasashe dari da ashirin da takwas ne suka kada kuri'un kin yarda da sauya matsayin birnin kudus, sai kasashe talatin da biyar  suka ki kada kuri'ar.

Tun da fari shugaban kasar Amurka ya yi wa duk wata kasa da ta ki amincewa da manufarsa barazanar yanke kudaden taimako.

3675336   

 

captcha