IQNA

23:52 - December 25, 2017
Lambar Labari: 3482236
Bangaren kasa da kasa, Justin Trudeau firayi ministan kasar Canada ya bayyana musulmin kasar da cewa suna da gagarumar rawar da suke takawa wajen ci gaban kasarsa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na aboutislam ya habarta cewa, a lokacin da yak egabatar da jawabia  gaban taron musulmin kasarsa, firayi ministan kasar Canada ya bayyana musulmin kasar da cewa suna da gagarumar rawar da suke takawa wajen ci gaban kasarsa a dukkanin bangarori.

Ya ce a cikin tsawon shekaru masu yawa, musulmi sun taka gagarumar rawa a dukkanin bangarori na ci gaban kasar, musamman a banfarori na ilimi da harkokin tattalin arziki.

A ranar Juma'a  ada ta gabata ce dai musulmi suka gudanar da babban taronsu na arewacin Amurka, wanda ya hada da musulmi daga ickin Amurka da kuma kasar Canada.

Babbar manufar wannan taron dai it ace kara wayar da kan musulmi kan muhimamn lamurran da suke a gabansu da kuma yadda ya kamata su mayar da hankali wajen ganin sun karfafa alakarsu da sauran jama'a tare da nuna musu cewa msuulunci addinin zaman lafiya ne.

Dubban musulmi ne dai suka halarci wanna zaman taron wanda ya hada har da manyan shugabannin kungiyoyin musulmi na cikin Amurka da kuma Canada, kamar yadda wasu jami'a na kasashen biyu ma sun halarci wurin.

3675589

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، cewa ، canada ، Justin Trudeau ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: