Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Alsharq ta kasar Qatar cewa, ana shirin gudanar da baje kolin mai taken tarihin Andalus a kasar Qatar a cikin shekara mai kamawa tare da halartar bangarorin kasashen biyu.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan baje koli cibiyar raya al’adun Andalus tana gudanar da shia kowace sekara, amma a wannan karn za a gudanar da shi ne a yankin Kitara na kasar Qatar.
Hakan ya biyo bayan wata yarjejeniyar da bangarorin byu suka cimmawa ne, inda aka ajiye a kan cewa a shekara mai kamawa za a gudana da wannan baje koli kamar yadda aka saba, amma a wannan ka a kasar Qatar.
Cibiyar kula da harkokin al’adu ta kasar Qatar ita ce za ta dauki nauyin dukkanin kudaden da za a kasha wajen gudanar da wannan baje koli a kasar.