Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalt daga shafin tashar Almanar cewa, a yau an fara gudanar da zaman taro na kafofin yada labarai na kasashen musulmi a birnin Beirut na Lebanon kan batun Quds tun bayan da Trump ya yi klaman amincewa da birnin a matsayin fadar mulkin yahudawa.
Bayanin y ace wannan zaman taro na kafofin yada labarai na kasashen musulmi ya mayar da hankali ne kan irin matakan da za su dauka wajen mayar da hankali kan batun na Quds da kuma yadda ya kamata musulmi su zama cikin fadaka dangane da hadarin da wannan birnin da kuma masallaci mai alfara suke ciki.
‘Yan jarida 200 ne suke halartar wannan zaman taro daga kasashen larabawa da kuma na musulmi daban-daban.