IQNA

Mutane 14 Sun Rasa Rayukansu A Wani Hari Da Aka Kai Najeriya

23:42 - January 03, 2018
Lambar Labari: 3482265
Bangaren kasa da kasa, akalla mutane  14 ne aka tabbatar da rasuwarsu sakamakon wani harin ta’addanci da aka kai a wani masallaci a gain Gamboru.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sporting cewa, akalla mutane 14 ne aka tabbatar da rasuwarsu sakamakon wani harin ta’addanci da aka kai a wani masallaci a gain Gamboru da ke cikin jahar Borno arewa maso gabacin Najeriya.

Shedun gani da ido sun ce da ta’addan da yake dauke da bama-baman ya shiga cikin sahun masallata  alokacin sallar asubahin yau, inda ya tarwatsa kantsa a tsakiyar masallata.

Mai gadin masallacin ya bayyana cewa, dukkanin mutanen da suke cikin masallaci a lokacin da ake salla sun rasa rayukansu, in banda ladanin masallacin shi kadai ne ya tsira.

Har yanzu dai babu wata kungiyar da ta sanar da cewa it ace ke da alhakin kaddamar da wannan hari na ta’addanci, amma dai ana nuna yatsan tuhuma ga kungiyar wahabiyawa ta boko haram wadda ta saba kaddamar da irin wadannan hare-hare a kan masallatai da kuma sauran wuraren gwamnati da na jama’a.

3679004

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna
captcha