IQNA

An Sace Wani Alkali Musulmi A Najeriya

16:48 - January 06, 2018
Lambar Labari: 3482273
Bangaren kasa da kasa, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun sace wani alkali musulmi a cikin jahar Niger da ke tarayyar Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na punchng cewa, Abubakar Jibrin alkali na gundumar Jermiya a cikin jahar Niger, wanda wasu 'yan bindiga suka sace a shekaran jiya a lokacin da yake dawowa daga wurin aikinsa.

Wannan danyen aiki ya zo ne 'yan kwanaki bayan sace wasu musulmi bakwai a lokutan baya tare da kashe wasu uku a wannan yanki.

Ibrahim Saleh shi ne dagacin yankin, ya kuma tabbatar da wannan labara, inda ya ce 'yan bindigar suna son a biya kudi har Naira miliyan 50 kafin su saki wannan alkali.

Ya ce wannan lamarin ya saka tsoro da firgici a cikin zukatan mazauna yankin.

Mahmud Abubakarshi ne jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda na yankin, ya bayyana cewa suna bin kadun lamarin.

3679404

 

 

captcha