Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa, a jiya ne Farfesa Rahmatulah Jian Mbang shugabar jami’ar Tais a birnin Dakar na Senegal ta gana da wata tawagar kasar Iran da ta ziyarci wannan jami’a.
A yayin ganawar an tattauna muhimamn lamurra da suka shafi harkokin bunkasa ilimia tsakanin kasashen biyu, da hakan ya hada da batun bude tsangayar koyar da ilimin sanin al’adu da tarihin kasar Iran.
Daga cikin abubuwan da za a rika koyarwa kuwa har da bincike kan irin dimbin rubuce-rubuce da masana suka yi a kasar Iran a tsawon tarihi, musamman wadanda suka shai addinin muslunci.
Baya ga haka kuma za a bayar da dama ga masu bincike daga bangarorin kasashen biyu da su rika ziyarar cibiyoyin ilimi na kasashe domin gudanar da bincike da kuma fadada ilimi.
Farfesa ta kara da cewa, akwai abubuwa da dama da suka hada mahangar Iran da Senegal ta fuska addinin, musamman kasatuwar Iran mabiya mazhabar ahlul bait (AS) yayin da kuma mafi yawan al’ummar Senegal mabiya darikun sufaye ne, wanda kuma asalin dariku da tafarkin ahlul bait duk abu daya ne.
Daga karshe an bayar da kyautar kur’ani da Abul kasim Fakhri ya tarjama a cikin harshen faransanci ga wannan babbar malama ta kasar Senegal.