Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na philly.com ya habarta cewa, mabiya addinin musuluci mazauna birnin Cherry Hill na jahar New Jersey a kasar Amurka za su gudanar da wani shiri na isar da sakon musulunci ga makwabtansu mabiya sauran adinai.
Muqaddas Ijaz daya daga cikin jagororin musulmi a garin na Cherry Hill ya bayyana cewa, su ne suka shirya wannan shiri tare da hadin gwiwa da shugabannin babban dakin karatu na birnin.
Ya ce babbar manufar hakan ita ce kara dankon zumunci tsakanin msuulmi da kuma wadanda ba musulmi, da kuma kara samar da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakaninsu.
Shirin dai ya hada da gayyatar sauran mabiya addinai zuwa gidajen musulmi da kuma cibiyoyinsu gami da wuraren badarsu da suka hada da masallatai da makarantu, domin ganin yadda musulmi suke yin adininsu, da kuma amsa tambayoyin jama’a da suke bukatar sanin wani abu dangane da musulmi da addininsu.
Kimanin musulmi dubu 6 ne dai suke rayuwa a cikin jahar New Jersey, wato kashi daya na mutaen jahar, kuma suna zaune afiya tare da kowa, mafi yawansu suna a garin Paterson ne.