Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Aldastur ta kasar Jordan cewa, a cikin shekara ta 2010 ne majalisar dinkin duniya ta ware makon farko na watan Fabrairi a matsayin makon fahimtar juna tsakanin addinai.
Bayanin ya ce a wannan makon mabiya addinai da suka hada da msuulmi da kuma kiristoci da yahudawa sun gudanar da taruka a wurare daban-daban a kasar Jordan, domin kara samun fahimtar juna da girmama fahimtar juna.
Majalisar dinkin duniya ta ware wannan ranar ne domin tabbatar da cewa al'umma sun girmama juna duk da irin banbamcin da ake akwai a tsakaninsu na addini da akida da kuma al'adu.
Wannan shiri yana samun karbuwa da tasiri matuka a cikin kasashe masu tasowa, musamman ma gtanin cewa a cikin lokutan nan ana samun matsaloli sakamakon bullar masu tsatsauran ra'ayi a dukkanin bangarorin addinai.