IQNA

Jami’an Tsaro Na Yin Leken Asiri Kan Musulmi Ta Hanyar Yanar Gizo A Amurka

22:24 - February 08, 2018
Lambar Labari: 3482377
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Amurka suna yin amfani da wani tsari ta hanyar yanar gizo wajen yin leken asiri a kan musulmi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na WCVB Boston cewa, jami’an tsaron kasar Amurka suna yin amfani da wani tsari ta hanyar yanar gizo mai suna (Geofeedi) wajen yin leken asiri a kan muuslmi a birnin Boston.

Bayanin ya ci gaba da cewa tsarin ya fara aiki ne gadan-gadan a tsakanin shekarun 2014 da 2016, ind ake sanya ido matuka  akan dukkanin harkokin musulmi da kai komonsu a cikin birnin da ma wasu yankuna.

Babbar manufar hakan ita ce yin liken asiri a kansu da kuma takura musu, da suna daukar matakan yaki da ta’addanci.

Wasu daga cikin kungiyoyin farar hula na Amurka sun soki gwamnatin kasar kan wannan tsari, inda suke ganin hakan yana a matsayin take hakkokin musulmi a matsayinsu na ‘yan kasa, wadanda suke da hakkin su yi addininsu yadda suka fahimta kuma suka imani, ba tare da an takura sub a.

Kungiyoyin sun bukaci da janye wannan tsari kuma  abayar da kariya ga musulmi a kan masu son cutar da su.

Wannan lamari dai ya kara kamari tun bayan hawan sabuwar gwamnatin kasar, wadda ta zo da taken kyamar musulmi da kuma baki a kasar.

3689883

 

 

captcha