IQNA

Mahangar Tsohon Mai bayar Da Fatawa Na Masar Kan Kur’ani Lokacin Manzo

23:21 - February 25, 2018
Lambar Labari: 3482427
Bangaren kasa da kasa, Ali Juma’a tsohon muftin kasar Masar ya bayyana cewa’anin da ke akwai lokacin manzon Allah yana da nakasu a cikin rubutunsa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da ake zantawa da shi a tashar talabijin ta CBC ta kasar Masar a jiya, Ali Juma’a tsohon muftin kasar Masar ya bayyana cewa’anin da ke akwai lokacin manzon Allah yana da nakasu a cikin rubutunsa da kuma jerin ayoyinsa da surorori.

Ya ce a lokacin manzo kur’ani bas hi da alamu da wasulla da kuma digagga, kamar yadda ayoyinsa da surorinsa a jere suke ba, wanda daga bisani ne aka yi aikin tsara su.

Ya kara da cewa kur’anin da ke akwai lokacin manzo babu sunayen surori a cikinsa a rubuce, ana fadinsu ne kawai da baki amma ba a rubuce ba.

Da dama daga cikin malami masu bincike sun ce an hada ayoyin kur’ani a lokacin manzo, amma bayan rasuwarsa a lokacin halifa na uku ne aka hada kur’anai domin kada a samu banbancin kwafin da ke hannun mutane a biranen musulmi.

3694367

 

 

 

 

captcha