Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran INA ya bayar da rahoton cewa, wannan zaman taron an kmamala shi a jiya a birnin Vienna na kasar Austria tare da halartar manyan mutane 250 da suka hada da manyan malaman addinai daban-daban, da suka hada da na muslunci da kiristanci.
Babban abin zaman taron ya mayar da hankalia kansa dai shi ne, tattaunawa da samar da fahimtar juna tsakanin dukkanin addinai, da kuma girmama mahanga da zaman lafiya.
Baya ga haka kuma an tattauna batun yanar gizo da kuam tasirinta wajen isar da sakonni da haka kan jama'a, idan aka yi amfani da wanann hanya ta yadda ya dace, kamar yadda kuma za ta iya zama hanyar hada husuma a tsakanin al'ummomi da addinai.
Dukkanin mahalarta taron sun yi iamnin cewa, dole ne a samu fahimtar juna a tsakanin al'ummomi, kuma hanyar tattaunawa ita kadai ce hanyar warware matsaloli ba kada kugen yaki a kan kasashe ko al'ummomi ba saboda dalilai na siyasa.