IQNA

23:45 - April 30, 2018
Lambar Labari: 3482616
Bangaren kur'ani, Haruna Mamadou Hassan daga jamhuriyar Nijar daya ne daga cikin wadanda suka halarci gasar kur'ani ta duniya ta daliban jami'a musulmi a birnin Mashhad na kasar Iran wanda kuma ya nuna kwazo matuka a gasar inda ya zo na biyu a bangaren harda.

 

Haruna Mamadou Hassan a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayyana cewa, hakika gudanar da gasar kur'ani mai tsarki na da matukar muhimamnci wajen kara karfafa gwiwar makaranta da mahardata.

Ya ce tun kafin wannan lokaci ya halarci wasu tarukan gasar kur'ani da aka yi a Iran, wannan shi ne karo na hudu, kuma a kowane lokaci ya zo ya kan ga komai ya canja ta fuskar ci gaban da ake samu a bangaren tsarion gasar da kuma gudanar da ita.

Dangane da nasarar da ya samu wajen wannan gasa inda ya zo matsayi na biyu a bangaren harda, ya bayyana cewa hakan abin farin ciki ne a gare shi da ma al'ummar kasarsa baki daya.

Dangane yadda ake gudanar da karatu a jamhuriyar Nijar ta fiskar kur'ani kuwa, ya bayyana cewa akwai hanyoyi daban-daban da ke bi, amma mafi yawa bisa ga al'ada akan fara ne da karatun allo, ta yadda dalibi zai rika rubuta kur'ani da kansa har ya saba, kuma ta haka babbaku suna zauna masa baya mantawa.

Ya ce daga bisani kuma a kan bi hanyoyi irin na koyarwa ta zamani wajen karatu da ma harda, wanda akasarin makarantun Islmiyya a halin yanzu irin wannan tsarin suke bi, amma duk da haka bai hana ci gaba da bin wancan tsohon tsarin da aka gada da kaka da kakanni  ba.

3710328

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، akwai ، karatu ، zamani ، hanyoyi ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: