IQNA

Rubutun Kwafin Kur’ani Mafi Girma A Masar

23:52 - May 05, 2018
Lambar Labari: 3482633
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Abdulsattar dan shekaru 41 khatibi a ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ya fara gudanar da wani aikin rubutun kur’ani mafi girma.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na mobtada.com cewa, Muhammad Abdulsattar ya fara gudanar da wannan aiki ne tun fiye da watanni biyu da suka gabata.

Bayanin ya ce wannan kur’ani zai zama shi ne mafi gima a duniya idan aka kammala aikinsa, domin kuwa ana gudanar da shi ne ta yadda zai zama shi ne irinsa a tarihinsa musulunci, ta fuskar girma, wanda tsawonsa ya kai mita 9, sannan kuma fadinsa ya kai mita 6 baki daya.

Ya ce da farko ya fuskanci matsalar wurin da ya kamata ya gudanar da wannan aiki, kasantuwar akwai bukatar wuri mai fadi wanda zai isa a baje yadukan da ake rubutua  kansu, amma daga karshe dai ya samu wurin masallacin Mait Gama a cikin lardin Dehqaliyya, inda  anan yake a halin yanzu.

Sa’annan kuma yana yin amfani da bakin yadi ne wajen rubutun wannan kur’ani, gami da farin fenti, kamar yadda kuma yake yin amfani da iliminsa n sanin fasahar rubutun larabaci, wanda hakan ya taimaka masa wajen kayata aikin nasa.

3711253

 

 

 

 

captcha