IQNA

Gasar Kur’ani Da Kiran Salla A Kasar Ghana

23:54 - May 05, 2018
Lambar Labari: 3482634
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gasar kur’ani da kiran salla a kasar Ghana wadda mutane 36 suka kara.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki gami da kiran salla a kasar Ghana, wadda cibiyar Imam Sadeq (AS) gami da cibiyar Fathul mubin suka dauki nauyin gudanarwaa  garin Tamale na kasar ta Ghana.

Shugaban karamin jakadancin Iran a Ghana Muhammad Hassan Ipekchi na daga mahalarta wurin bude taro gasar,wadda aka gudanar domin murnar zagayowar maulid Imam Zaman.

Sheikh Muhammad Tijani daya daga cikin malaman addini na kasar yana daga cikin wadanda aka gayyata domin bude zaman taron gasar.

Daga karshe dai za a sanar da sunayen wadanda suka zo a mataki na daya da na biyu da na uku a dukkanin bangarorin karatu da kuma hada gami da kiran salla.

3711430

 

 

 

 

captcha