IQNA

23:51 - May 06, 2018
Lambar Labari: 3482637
Bangaren kasa da kasa, Yusuf bin Ahmad Alusaimin babban sakataren kungiyar OIC ya bayyana cewa dole ne a mayar da musulmin Rohingya zuwa gidajensu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawwabatul Arab cewa, Yusuf bin Ahmad Alusaimin babban sakataren kungiyar OIC ya bayyana cewa dole ne babu wani dalili da zai sanya a ci gaba da barin muuslmin Rohingya  akasar bangaladesh, ya kamata su koma gidajensu.

Ya bayyana hakan ne a taron ministocin harkokin wajen kasashen musulmin da ake gudanarwa  a kasar ta Bangaladash, inda ya ce wakilan kasashen hamsin da bakawai da suka halarci wurin sun cimma matasaya kan wajabcin bayar da kariya ga musulmin na Rohingya.

Tare kuma da tababtar da cewa an mayar da su gidajensu tare da biyansu dukkanin hakkokinsu da aka haramta musu a matsayinsu na 'yan kasar Myanmar.

An gudanar da zaman taron ministocin harkokin wajen kasashen musulmi a birnin Daka na Bangaladesh mai taken sulhu da zaman lafiya.

3711805

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، bangaladash ، rohingya ، myanmar ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: