IQNA

23:54 - May 07, 2018
Lambar Labari: 3482640
Bangaren kasa da kasa, jiragen yakin masarautar Saudiyya sun kaddamar da hare-hare a kan ginin ofishin shugaban kasar Yemen a birnin San’a.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin barakish.net ya bayar da rahoton cewa, jiragen yakin masarautar Al Saud sun kai hare-haren ne a lokacin da shugaban majalisar koli ta siyasa a kasar Yemen Mahdi Mashat yake isowa.

Rahoton ya tabbatar da mutuwar mutuwar mutane shida tare da jikkatar wasu fiye da talatin sakamakon harin.

An jami’an tsaro suna dauke gawawwakin wadanda suka rasu da kuma wadanda suka jikkata, kuma ha yanzu babu bayani kan makomar Mahdi Moshat, amma wasu majiyoyin na kusa da majalisar koli ta siyasar kasar sun ce yana cikin koshin lafiya.

3712173

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: