IQNA

23:56 - May 12, 2018
Lambar Labari: 3482651
Bangaren kasa da kasa, cibiyar yada al'adun muslunci ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da harin ta'addancin da aka kai kan masallacin Imam Hussain (AS) a garin Durban na Afirka ta kudu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a cikin bayanin da ta fitar, babbar cibiyar yada al'adun muslunci ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da harin ta'addancin da aka kai kan masallacin Imam Hussain (AS) a garin Durban a Afirka ta kudu a rewacin kasar.

Bayanin ya ce ko shakka babu wannan harin ta'addancin aiki ne na makiya da suke da mummunar manufar hada musulmi fada da junansu, amma mabiya mazhabar ahlul bait (AS) ba za su taba fadawa cikin wannan tarko na makiya ba.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da yadda wasu daga cikin musulmi abin takaici suka zama 'yan koren yahudawa  makiya musulmi da suke daukar nauyin irin wadannan ayyuka na ta'addan tare da bakanta sunan addinin musluncia  idon duniya.

3713506

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: