IQNA

21:50 - May 17, 2018
Lambar Labari: 3482668
Bangaren kasa da kasa, an bayyana cewa babu wani tasirin da zaman kungiyar hadin kan kasashen Larabawa zai yi dangane da matsalar da Palasdinu ta shiga a halin yanzu.

 

Kamfanin dillacin labaran iqna ya habarta cewa, a zantawarsa da gidan radiyon Sputnik kan zaman gaggawa da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa suka kira a jiya Laraba da kuma wanda zasu gudanar a nan gaba, tsohon jami'in jakadancin kasar Masar ya bayyana cewa, Babu wani abin da zaman zai haifar illa yin tofin Allah tsine kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Haka nan kuma ya kara da cewa, Tun a lokacin da shugaban kasar Amurka ya shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila ya dace kungiyar kasashen Larabawa su dauki matakin kalubalantarsa amma a halin yanzu da lokaci ya kure musu babu wani tasirin da zasu yi kan matsalar. 

3714952

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، larabawa ، Palastine ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: