IQNA

23:48 - May 19, 2018
Lambar Labari: 3482673
Bangaren kasa da kasa, an cimma wata yarjejeniya tsakanin mahukuntan kasar Saiyo da Iran kan bayar da taimako ga daliban jami’a musulmi a kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata ganawa da aka gudanar sakanin shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a Saliyo da kuma shugaban jami’ar Milti Magay ta kasar Muhammad Tabita Kamara, an cimma matsaya kan bayar da taimako ga daliban jami’a musulmi nakasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan yarjejeniya ta kunshi bayar da dama ga daiban jami’a muuslmi na kasar Saliyo su samu taimako na abubuwan da suke bukata a lokacin karatuns daga cibiyar raya al’adun musulunci ta kasar Iran.

Haka nan kuma wannan yarjejeniya ta kunshi bayar da damar samar da guraben karatu a dukkanin bangarori na ilimin kimiyya da fasaha a jami’oin Iran ga dalibai musulmi ‘yan kasar Saliyo.

Ma’aikatar ilimi ta kasar Saliyo ta yi lale marhabin da wannan yunkuri na kasar Iran, tare da bayyana hakan a matsayin wata babbar dama wadda ba kasafai ake samun irin ta ba.

3715714

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، yunkuri ، Saliyo ، Iran ، yarjejeniya ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: