IQNA

23:44 - May 23, 2018
Lambar Labari: 3482686
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Indonesia ta hana yahudawan sahyuniya shiga cikin kasarta sakamakon kisan kiyashin da Isra’ila take yi wa Palastinawa.

Kamfanin dillancin labaran ina ya habarta cewa, jaridar Al-nahar ta bayar da rahoton cewa, Emmanuel Nashon kakakin ma’aikatar harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila ya sanar da cewa, Indonesia ta haramta bayar da visa ga duk wani bayahuden Isra’ila.

Kakakin ma’aikatar harkokin Isra’aila ya sheda wa jaridar yadiot Ahranut cewa, suna yin kokarinsu domin ganin sun jawo hankalin Indonesia, domin ta janye wannan matakin.

Tun kimanin makonni biyu da suka gabata ne dai Indonesia ta fitar da bayani da a cikinsa ta yi Allawadai da Isra’ila, kan kisan kiyashin da take yi kan al’ummar Palastine ba ji ba gani.

Daga karshen watan Mayun da ya gabata ya zuwa yanzu sojojin Isra’ila sun harbe Falastinawa kusan saba’in har lahira, tare da jikkata wasu dubbai.

3716910

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: