IQNA

23:36 - May 30, 2018
Lambar Labari: 3482706
Bangaren kasa da kasa, an shirya gasar kur’ani mai tsarki a birnin Damascus na Syria tsakanin ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasa da kuma karamin ofishin jakadancin Iran.

 

Kamfanin dillacin labaran iqna ya habarta cewa, an shirya gasar kur’ani mai tsarki a birnin Damascus na Syria tsakanin ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasa da kuma karamin ofishin jakadancin Iran da ke kasar ta Syria.

Abul Fad Salehi shi ne shuagaban karamin ofishin jakadancin Iran a Damascus, wanda kuma shi ne ya fara bude taron karatun kur’ani mai tsarki.

Muhammad Uns Dawamina shi ne shugaban cibiyar hardar ur’ani ta Assad, ya gabatar da jawabi dangane da gasar da kuma bangarorin da za ta kunsa, kama yadda shi ma Ref’at Ali Adib ministan ma’aikatar kula da harkokin addini na kasar ya gabatar da nasa jawabin.

Muhammad Ali Hamdu shi ne ya fara gabaar da karatu daga cikin masu halartar gasar, wada ya fito daga garin Aleppo, kamar yaddada sauran masu gasar suka fito daga sassa na Syria.

Daga karshen gasar za a bayar da kyautuka ne ga dukkanin bangarori na harda da tilawa da kuma tajwidi.

3718983

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، tilawa ، Damascus ، Syria ، Iran ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: