Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka kawo karshen gasar kur’ani mai tsarki ta daliban makarantun firamare da sakandare a birnin Acra na kasar Ghana karo biyar, wadda aka saba gudanarwa a cikin watan azumi.
Kasar Iran ce dai take daukar nauyin wannan gasa, wadda ta hada daliban makarantun addini da kuma na book, inda gasar kan mayar da hankali a bangaren harda da kuma kira’a.
Makarantun Rashad, da Imam Mahdi (AJ) da kuma makarantar Al-adab su ne suka zo na daya da na biyu da kuma na uku.
Wasu daga cikin manyan malaman kasar sun halaci taron rufe gasar, da suka hada da sheikh Nurul Haq Yahuza, da kuma Sheikh Muhammad Mujib, mataimakin darakta mai kula da harkokin addini a jami’oin kasar.