Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin Bawabah news ya habarta cewa kimanin dalibai 35 suka samu nasarar lashe gasar kur'ani da aka gudanar a lardin Jiza na kasar masar wadanda suka samu karramawa ta musamman.
An gudanar da gasar ne bisa kulawar cibiyar Azhar inda sheikh Abdullah Hesham ya jagoranci gasar wadda aka gudanara yankin Umraniya na gundumar Jizah.
Mahmud kamal Dali da shekh Hesham Abdullah da kuma wasu jami'ai da malamai sun halarci wannan wuri tare da mika kyautukan da aka yi tanadi ga wadanda suka nuna kwazo.